Hausa
Surah Ad-Dukhan ( The Smoke ) - Aya count 59
حم
( 1 ) Ḥ. M̃.
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ
( 2 ) Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani.
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ ۚ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ
( 3 ) Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi.
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ
( 4 ) A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne.
أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا ۚ إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
( 5 ) Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã.
رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ ۚ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
( 6 ) Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani.
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ
( 7 ) (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka).
لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۖ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ
( 8 ) Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko.
بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ
( 9 ) A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka.
فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاءُ بِدُخَانٍ مُّبِينٍ
( 10 ) Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne.
يَغْشَى النَّاسَ ۖ هَٰذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ
( 11 ) Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi.
رَّبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ
( 12 ) Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne.
أَنَّىٰ لَهُمُ الذِّكْرَىٰ وَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ
( 13 ) Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)?
ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ
( 14 ) Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci."
إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا ۚ إِنَّكُمْ عَائِدُونَ
( 15 ) Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin).
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَىٰ إِنَّا مُنتَقِمُونَ
( 16 ) Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne.
وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءَهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ
( 17 ) Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu.
أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ ۖ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ
( 18 ) (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku."
وَأَن لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ ۖ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ
( 19 ) "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne."
وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ
( 20 ) "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni."
وَإِن لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ
( 21 ) "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni."
فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَٰؤُلَاءِ قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ
( 22 ) Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi.
فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ
( 23 ) (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)"
وَاتْرُكِ الْبَحْرَ رَهْوًا ۖ إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ
( 24 ) "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa."
كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
( 25 ) Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari.
وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ
( 26 ) Da shuke-shuke da matsayi mai kyau.
وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ
( 27 ) Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu.
كَذَٰلِكَ ۖ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ
( 28 ) Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam.
فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ
( 29 ) Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba.
وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ
( 30 ) Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa.
مِن فِرْعَوْنَ ۚ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ
( 31 ) Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna.
وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَىٰ عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ
( 32 ) Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne.
وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاءٌ مُّبِينٌ
( 33 ) Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna
إِنَّ هَٰؤُلَاءِ لَيَقُولُونَ
( 34 ) Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa,
إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ
( 35 ) "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba."
فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
( 36 ) "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya."
أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ أَهْلَكْنَاهُمْ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ
( 37 ) shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi.
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ
( 38 ) Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã.
مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
( 39 ) Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba.
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ
( 40 ) Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya.
يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
( 41 ) Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba.
إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ ۚ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ
( 42 ) fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
إِنَّ شَجَرَتَ الزَّقُّومِ
( 43 ) Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã),
طَعَامُ الْأَثِيمِ
( 44 ) Ita ce abincin mai laifi.
كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ
( 45 ) Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna.
كَغَلْيِ الْحَمِيمِ
( 46 ) Kamar tafasar ruwan zãfi.
خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَىٰ سَوَاءِ الْجَحِيمِ
( 47 ) (A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm."
ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ
( 48 ) "Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi."
ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ
( 49 ) (A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!"
إِنَّ هَٰذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ
( 50 ) "Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi."
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ
( 51 ) Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce.
فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
( 52 ) A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari.
يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ
( 53 ) Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna.
كَذَٰلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ
( 54 ) Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu.
يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ
( 55 ) Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro).
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَىٰ ۖ وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ
( 56 ) Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm.
فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ۚ ذَٰلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ
( 57 ) Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma.
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
( 58 ) Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa.
فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ
( 59 ) Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne.