Hausa
Surah Al-Waqi'ah ( The Event ) - Aya count 96
إِذَا وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ
( 1 ) Idan mai aukuwa ta auku.
لَيْسَ لِوَقْعَتِهَا كَاذِبَةٌ
( 2 ) Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta.
خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ
( 3 ) (Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa.
إِذَا رُجَّتِ الْأَرْضُ رَجًّا
( 4 ) Idan aka girgiza ƙasã girgizwa.
وَبُسَّتِ الْجِبَالُ بَسًّا
( 5 ) Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa.
فَكَانَتْ هَبَاءً مُّنبَثًّا
( 6 ) Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa.
وَكُنتُمْ أَزْوَاجًا ثَلَاثَةً
( 7 ) Kuma kun kasance nau'i uku.
فَأَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ
( 8 ) Watau mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
وَأَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ مَا أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ
( 9 ) Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu?
وَالسَّابِقُونَ السَّابِقُونَ
( 10 ) Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan,
أُولَٰئِكَ الْمُقَرَّبُونَ
( 11 ) Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar.
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ
( 12 ) A ckin Aljannar ni'ima.
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ
( 13 ) Jama'a ne daga mutãnen farko.
وَقَلِيلٌ مِّنَ الْآخِرِينَ
( 14 ) Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe.
عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوْضُونَةٍ
( 15 ) (Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙuu.
مُّتَّكِئِينَ عَلَيْهَا مُتَقَابِلِينَ
( 16 ) Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna.
يَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ
( 17 ) Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu.
بِأَكْوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ
( 18 ) Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga.
لَّا يُصَدَّعُونَ عَنْهَا وَلَا يُنزِفُونَ
( 19 ) Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa.
وَفَاكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ
( 20 ) Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe.
وَلَحْمِ طَيْرٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
( 21 ) Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa.
وَحُورٌ عِينٌ
( 22 ) Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu.
كَأَمْثَالِ اللُّؤْلُؤِ الْمَكْنُونِ
( 23 ) Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye.
جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
( 24 ) A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa.
لَا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا تَأْثِيمًا
( 25 ) Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi.
إِلَّا قِيلًا سَلَامًا سَلَامًا
( 26 ) Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun.
وَأَصْحَابُ الْيَمِينِ مَا أَصْحَابُ الْيَمِينِ
( 27 ) Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma?
فِي سِدْرٍ مَّخْضُودٍ
( 28 ) (Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya.
وَطَلْحٍ مَّنضُودٍ
( 29 ) Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya.
وَظِلٍّ مَّمْدُودٍ
( 30 ) Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya.
وَمَاءٍ مَّسْكُوبٍ
( 31 ) Da wani ruwa mai gudãna.
وَفَاكِهَةٍ كَثِيرَةٍ
( 32 ) Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa.
لَّا مَقْطُوعَةٍ وَلَا مَمْنُوعَةٍ
( 33 ) Bã su yankẽwa kuma bã a hana su.
وَفُرُشٍ مَّرْفُوعَةٍ
( 34 ) Da wasu shimfiɗu maɗaukaka.
إِنَّا أَنشَأْنَاهُنَّ إِنشَاءً
( 35 ) Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa.
فَجَعَلْنَاهُنَّ أَبْكَارًا
( 36 ) Sa'an nan Muka sanya su budurwai.
عُرُبًا أَتْرَابًا
( 37 ) Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya.
لِّأَصْحَابِ الْيَمِينِ
( 38 ) Ga mazõwa dãma.
ثُلَّةٌ مِّنَ الْأَوَّلِينَ
( 39 ) Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko.
وَثُلَّةٌ مِّنَ الْآخِرِينَ
( 40 ) Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe.
وَأَصْحَابُ الشِّمَالِ مَا أَصْحَابُ الشِّمَالِ
( 41 ) Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu?
فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍ
( 42 ) Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi.
وَظِلٍّ مِّن يَحْمُومٍ
( 43 ) Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi.
لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ
( 44 ) Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba.
إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَٰلِكَ مُتْرَفِينَ
( 45 ) Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi.
وَكَانُوا يُصِرُّونَ عَلَى الْحِنثِ الْعَظِيمِ
( 46 ) Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma.
وَكَانُوا يَقُولُونَ أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَإِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
( 47 ) Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan?"
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ
( 48 ) "Shin, kuma da ubanninmu na farko?"
قُلْ إِنَّ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ
( 49 ) Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe."
لَمَجْمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَاتِ يَوْمٍ مَّعْلُومٍ
( 50 ) "Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne."
ثُمَّ إِنَّكُمْ أَيُّهَا الضَّالُّونَ الْمُكَذِّبُونَ
( 51 ) "Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa!"
لَآكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ
( 52 ) "Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã)."
فَمَالِئُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ
( 53 ) "Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta."
فَشَارِبُونَ عَلَيْهِ مِنَ الْحَمِيمِ
( 54 ) "Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi."
فَشَارِبُونَ شُرْبَ الْهِيمِ
( 55 ) "Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa."
هَٰذَا نُزُلُهُمْ يَوْمَ الدِّينِ
( 56 ) Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako.
نَحْنُ خَلَقْنَاكُمْ فَلَوْلَا تُصَدِّقُونَ
( 57 ) Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba?
أَفَرَأَيْتُم مَّا تُمْنُونَ
( 58 ) Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi?
أَأَنتُمْ تَخْلُقُونَهُ أَمْ نَحْنُ الْخَالِقُونَ
( 59 ) Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa?
نَحْنُ قَدَّرْنَا بَيْنَكُمُ الْمَوْتَ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ
( 60 ) Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa ba,
عَلَىٰ أَن نُّبَدِّلَ أَمْثَالَكُمْ وَنُنشِئَكُمْ فِي مَا لَا تَعْلَمُونَ
( 61 ) A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba.
وَلَقَدْ عَلِمْتُمُ النَّشْأَةَ الْأُولَىٰ فَلَوْلَا تَذَكَّرُونَ
( 62 ) Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba?
أَفَرَأَيْتُم مَّا تَحْرُثُونَ
( 63 ) Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa?
أَأَنتُمْ تَزْرَعُونَهُ أَمْ نَحْنُ الزَّارِعُونَ
( 64 ) Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa?
لَوْ نَشَاءُ لَجَعَلْنَاهُ حُطَامًا فَظَلْتُمْ تَفَكَّهُونَ
( 65 ) Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki.
إِنَّا لَمُغْرَمُونَ
( 66 ) (Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra!"
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ
( 67 ) "Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa!"
أَفَرَأَيْتُمُ الْمَاءَ الَّذِي تَشْرَبُونَ
( 68 ) Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha?
أَأَنتُمْ أَنزَلْتُمُوهُ مِنَ الْمُزْنِ أَمْ نَحْنُ الْمُنزِلُونَ
( 69 ) Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa?
لَوْ نَشَاءُ جَعَلْنَاهُ أُجَاجًا فَلَوْلَا تَشْكُرُونَ
( 70 ) Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa?
أَفَرَأَيْتُمُ النَّارَ الَّتِي تُورُونَ
( 71 ) Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa?
أَأَنتُمْ أَنشَأْتُمْ شَجَرَتَهَا أَمْ نَحْنُ الْمُنشِئُونَ
( 72 ) Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa?
نَحْنُ جَعَلْنَاهَا تَذْكِرَةً وَمَتَاعًا لِّلْمُقْوِينَ
( 73 ) Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji.
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ
( 74 ) Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma.
فَلَا أُقْسِمُ بِمَوَاقِعِ النُّجُومِ
( 75 ) To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri.
وَإِنَّهُ لَقَسَمٌ لَّوْ تَعْلَمُونَ عَظِيمٌ
( 76 ) Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani.
إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ
( 77 ) Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja.
فِي كِتَابٍ مَّكْنُونٍ
( 78 ) A cikin wani littafi tsararre.
لَّا يَمَسُّهُ إِلَّا الْمُطَهَّرُونَ
( 79 ) Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake.
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ
( 80 ) Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta.
أَفَبِهَٰذَا الْحَدِيثِ أَنتُم مُّدْهِنُونَ
( 81 ) Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa?
وَتَجْعَلُونَ رِزْقَكُمْ أَنَّكُمْ تُكَذِّبُونَ
( 82 ) Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi)?
فَلَوْلَا إِذَا بَلَغَتِ الْحُلْقُومَ
( 83 ) To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa).
وَأَنتُمْ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ
( 84 ) Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo.
وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنكُمْ وَلَٰكِن لَّا تُبْصِرُونَ
( 85 ) Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani.
فَلَوْلَا إِن كُنتُمْ غَيْرَ مَدِينِينَ
( 86 ) To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba?
تَرْجِعُونَهَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
( 87 ) Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya.
فَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُقَرَّبِينَ
( 88 ) To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta,
فَرَوْحٌ وَرَيْحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ
( 89 ) Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima.
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ
( 90 ) Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma,
فَسَلَامٌ لَّكَ مِنْ أَصْحَابِ الْيَمِينِ
( 91 ) Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma.
وَأَمَّا إِن كَانَ مِنَ الْمُكَذِّبِينَ الضَّالِّينَ
( 92 ) Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun,
فَنُزُلٌ مِّنْ حَمِيمٍ
( 93 ) Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi.
وَتَصْلِيَةُ جَحِيمٍ
( 94 ) Da ƙõnuwa da Jahĩm,
إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ الْيَقِينِ
( 95 ) Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni.
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ
( 96 ) Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangijinka, Mai karimci.