Hausa
Surah Al-Infitar ( The Cleaving ) - Aya count 19
إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ
( 1 ) Idan sama ta tsãge.
وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ
( 2 ) Kuma idan taurãri suka wãtse.
وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ
( 3 ) Kuma idan tẽkuna aka facce su.
وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ
( 4 ) Kuma idan kaburbura aka tõne su.
عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ
( 5 ) Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ
( 6 ) Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ
( 7 ) Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ
( 8 ) A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ
( 9 ) A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ
( 10 ) Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
كِرَامًا كَاتِبِينَ
( 11 ) Mãsu daraja, marubũta.
يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ
( 12 ) Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
( 13 ) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ
( 14 ) Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ
( 15 ) Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ
( 16 ) Bã zã su faku daga gare ta ba.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ
( 17 ) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ
( 18 ) Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا ۖ وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ
( 19 ) Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.