Hausa
Surah Al-Qiyamah ( The Resurrection ) - Aya count 40
لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ
( 1 ) Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ
( 2 ) Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَّجْمَعَ عِظَامَهُ
( 3 ) Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
بَلَىٰ قَادِرِينَ عَلَىٰ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ
( 4 ) Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
بَلْ يُرِيدُ الْإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ
( 5 ) Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ
( 6 ) Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?"
فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ
( 7 ) To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
وَخَسَفَ الْقَمَرُ
( 8 ) Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ
( 9 ) Aka tãra rãnã da watã
يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ
( 10 ) Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?"
كَلَّا لَا وَزَرَ
( 11 ) A'aha! bãbu mafaka.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ
( 12 ) zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ
( 13 ) Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
بَلِ الْإِنسَانُ عَلَىٰ نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ
( 14 ) Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
وَلَوْ أَلْقَىٰ مَعَاذِيرَهُ
( 15 ) Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ
( 16 ) Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ
( 17 ) Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ
( 18 ) To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ
( 19 ) sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ
( 20 ) A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ
( 21 ) Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ
( 22 ) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ
( 23 ) Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ
( 24 ) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ
( 25 ) Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
كَلَّا إِذَا بَلَغَتِ التَّرَاقِيَ
( 26 ) A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
وَقِيلَ مَنْ ۜ رَاقٍ
( 27 ) kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ
( 28 ) Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ
( 29 ) Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ
( 30 ) Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ
( 31 ) To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
( 32 ) Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰ أَهْلِهِ يَتَمَطَّىٰ
( 33 ) Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ
( 34 ) Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
ثُمَّ أَوْلَىٰ لَكَ فَأَوْلَىٰ
( 35 ) Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَن يُتْرَكَ سُدًى
( 36 ) Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمْنَىٰ
( 37 ) Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ
( 38 ) Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ
( 39 ) Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
أَلَيْسَ ذَٰلِكَ بِقَادِرٍ عَلَىٰ أَن يُحْيِيَ الْمَوْتَىٰ
( 40 ) Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?