Hausa
Surah An-Nazi'at ( Those who Pull Out ) - Aya count 46
وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا
( 1 ) Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi.
وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا
( 2 ) Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi.
وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا
( 3 ) Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا
( 4 ) Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre.
فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا
( 5 ) Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ
( 6 ) Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa.
تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ
( 7 ) Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye.
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ
( 8 ) Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ
( 9 ) Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ
( 10 ) Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu?
أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً
( 11 ) "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?"
قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ
( 12 ) Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!"
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ
( 13 ) To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ
( 14 ) Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ
( 15 ) Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?
إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى
( 16 ) A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ
( 17 ) Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰ أَن تَزَكَّىٰ
( 18 ) "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka.
وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ
( 19 ) "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?"
فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَىٰ
( 20 ) Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma.
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ
( 21 ) Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni),
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ
( 22 ) Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ
( 23 ) Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَىٰ
( 24 ) Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka."
فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَىٰ
( 25 ) Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ
( 26 ) Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَا
( 27 ) Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا
( 28 ) Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا
( 29 ) Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا
( 30 ) Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا
( 31 ) Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا
( 32 ) Da duwatsu, Yã kafe ta.
مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ
( 33 ) Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ
( 34 ) To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَىٰ
( 35 ) Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ
( 36 ) Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ
( 37 ) To, amma wanda ya yi girman kai.
وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا
( 38 ) Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya).
فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَىٰ
( 39 ) To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَىٰ
( 40 ) Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَىٰ
( 41 ) To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا
( 42 ) Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا
( 43 ) Me ya haɗã ka da ambatonta?
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَاهَا
( 44 ) Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.
إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا
( 45 ) Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا
( 46 ) Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.