Select reciter
Hausa
Surah At-Tariq ( The Night-Comer ) - Aya count 17
وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ
( 1 ) Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ
( 2 ) To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
النَّجْمُ الثَّاقِبُ
( 3 ) Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.
إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ
( 4 ) Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ
( 5 ) To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
خُلِقَ مِن مَّاءٍ دَافِقٍ
( 6 ) An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ
( 7 ) Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ
( 8 ) Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ
( 9 ) Rãnar da ake jarrabawar asirai.
فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ
( 10 ) Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ
( 11 ) Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ
( 12 ) Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa,
إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ
( 13 ) Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki
وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ
( 14 ) Kuma shĩ bã bananci bane
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا
( 15 ) Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
وَأَكِيدُ كَيْدًا
( 16 ) Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا
( 17 ) Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.