Hausa
Surah Abasa ( He frowned ) - Aya count 42
عَبَسَ وَتَوَلَّىٰ
( 1 ) Yã game huska kuma ya jũya bãya.
أَن جَاءَهُ الْأَعْمَىٰ
( 2 ) Sabõda makãho yã je masa.
وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّىٰ
( 3 ) To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَىٰ
( 4 ) Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَىٰ
( 5 ) Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّىٰ
( 6 ) Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ
( 7 ) To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
وَأَمَّا مَن جَاءَكَ يَسْعَىٰ
( 8 ) Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
وَهُوَ يَخْشَىٰ
( 9 ) Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ
( 10 ) Kai kuma kã shagala ga barinsa!
كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ
( 11 ) A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
فَمَن شَاءَ ذَكَرَهُ
( 12 ) Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ
( 13 ) (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ
( 14 ) Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
بِأَيْدِي سَفَرَةٍ
( 15 ) A cikin hannãyen mala'iku marubũta.
كِرَامٍ بَرَرَةٍ
( 16 ) Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ
( 17 ) An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ
( 18 ) Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ
( 19 ) Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ
( 20 ) Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ
( 21 ) Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
ثُمَّ إِذَا شَاءَ أَنشَرَهُ
( 22 ) Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ
( 23 ) Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَىٰ طَعَامِهِ
( 24 ) To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاءَ صَبًّا
( 25 ) Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا
( 26 ) Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا
( 27 ) Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
وَعِنَبًا وَقَضْبًا
( 28 ) Da inabi da ciyãwa.
وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا
( 29 ) Da zaitũni da itãcen dabĩno.
وَحَدَائِقَ غُلْبًا
( 30 ) Da lambuna, mãsu yawan itãce.
وَفَاكِهَةً وَأَبًّا
( 31 ) Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ
( 32 ) Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
فَإِذَا جَاءَتِ الصَّاخَّةُ
( 33 ) To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ
( 34 ) Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ
( 35 ) Da uwarsa da ubansa.
وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ
( 36 ) Da mãtarsa da ɗiyansa.
لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ
( 37 ) Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ
( 38 ) Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ
( 39 ) Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ
( 40 ) Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ
( 41 ) Baƙi zai rufe su.
أُولَٰئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ
( 42 ) Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).