Hausa
Surah Al-Mursalat ( Those sent forth ) - Aya count 50
وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا
( 1 ) Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا
( 2 ) Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا
( 3 ) Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا
( 4 ) sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا
( 5 ) Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا
( 6 ) Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ
( 7 ) Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ
( 8 ) To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
وَإِذَا السَّمَاءُ فُرِجَتْ
( 9 ) Kuma, idan sama aka tsãge ta.
وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ
( 10 ) Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ
( 11 ) Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ
( 12 ) Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
لِيَوْمِ الْفَصْلِ
( 13 ) Domin rãnar rarrabẽwa.
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ
( 14 ) Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 15 ) Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ
( 16 ) Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ
( 17 ) Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ
( 18 ) Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 19 ) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ
( 20 ) Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ
( 21 ) Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ
( 22 ) Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ
( 23 ) Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 24 ) Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا
( 25 ) Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
أَحْيَاءً وَأَمْوَاتًا
( 26 ) Ga rãyayyu da matattu,
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاءً فُرَاتًا
( 27 ) Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 28 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
انطَلِقُوا إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ
( 29 ) Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
انطَلِقُوا إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ
( 30 ) Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ
( 31 ) Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ
( 32 ) Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ
( 33 ) Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 34 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ
( 35 ) Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ
( 36 ) Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 37 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ
( 38 ) Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ
( 39 ) To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 40 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ
( 41 ) Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ
( 42 ) Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
( 43 ) (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa."
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ
( 44 ) Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 45 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ
( 46 ) (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne."
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 47 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ
( 48 ) Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba."
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
( 49 ) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ
( 50 ) To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni