Select reciter
Hausa
Surah Ad-Dhuha ( The Forenoon ) - Aya count 11
وَالضُّحَىٰ
( 1 ) Inã rantsuwa da hantsi.
وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ
( 2 ) Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
( 3 ) Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ الْأُولَىٰ
( 4 ) Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰ
( 5 ) Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَىٰ
( 6 ) Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَىٰ
( 7 ) Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَىٰ
( 8 ) Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ
( 9 ) Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ
( 10 ) Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ
( 11 ) Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).