Hausa
Surah An-Naba' ( The Great News ) - Aya count 40
عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ
( 1 ) A kan mẽ suke tambayar jũna?
عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ
( 2 ) A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ
( 3 ) Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
( 4 ) A'aha! Zã su sani.
ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
( 5 ) Kuma, a'aha! Zã su sani.
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا
( 6 ) Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا
( 7 ) Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا
( 8 ) Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا
( 9 ) Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا
( 10 ) Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا
( 11 ) Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا
( 12 ) Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا
( 13 ) Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا
( 14 ) Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
لِّنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا
( 15 ) Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا
( 16 ) Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا
( 17 ) Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا
( 18 ) Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا
( 19 ) Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا
( 20 ) Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا
( 21 ) Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
لِّلطَّاغِينَ مَآبًا
( 22 ) Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
لَّابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا
( 23 ) Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا
( 24 ) Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا
( 25 ) Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
جَزَاءً وِفَاقًا
( 26 ) Sakamako mai dãcẽwa.
إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا
( 27 ) Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا
( 28 ) Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا
( 29 ) Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا
( 30 ) Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا
( 31 ) Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا
( 32 ) Lambuna da inabõbi.
وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا
( 33 ) Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
وَكَأْسًا دِهَاقًا
( 34 ) Da hinjãlan giya cikakku.
لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا
( 35 ) Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا
( 36 ) Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
رَّبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرَّحْمَٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا
( 37 ) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرَّحْمَٰنُ وَقَالَ صَوَابًا
( 38 ) Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
ذَٰلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ ۖ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِ مَآبًا
( 39 ) Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا
( 40 ) Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!"